Aslm yan'uwa maza da mata mabiya wannan shafi mai albarka,
A YAU muna dauke da darasi akan waya kirar
ANDROID
Wayar android tana yin abubuwa da dama na ban
mamaki wadanda zama ka iya cewa karyane in har
baka ga anyi ba ko kuma an kwatanta maka yadda
ake yiba,
ILIMI KOGI NE. Ga kadan daga cikin abinda na sani cikin
abubuwan da android keyi,
Neman Mota: wayarka ta android zaka iya amfani
da ita wajen nemo motarka idan ta bace idan har
kafin ta bace kayi wannan setting din
Kulle/Bude Mota: xaka iya amfani da wayar android wajen kulle (lock) da kuma bude (unlock)
motarka tare da taimakon wani application
Kama Barawon Da Ya Sace Wayar:
Xaka iya amfani da wayar android wajen cabke
barawon da ya dauke maka wayar ta hanyar
bayyana maka lambar wayarsa wadda ya
sanya akan wayar,garinsu da unguwarsu.
Kulle Kanta: Wayar android xaka iya bata umurni
daga duk inda kake, misali tayi alarm, ko Ta kulle
kanta, ko tayi maka Backup na contact, ko tayi
restore na komai na cikinta.
Hana Kiran Wani: Da wayar android zaka iya zabar wanda kake so ya kira ka da wanda baka
son ya kiraka, zaka ware sakon daka ke so ya
shigo da wanda baka so ya shigo.
Auna Mai Na Mota: Da wayarka android Zaka iya
auna man ka domin kasan adadin man motar da
zai kai ka wani gari misali ABUJA kafin ka ka fara tafiya, za kayi lissafin man fetur, misali ka zuba man
fetur na N3000, sai kaje kan application din ka
rubuta mata adadin kudin da ka sayi man, nan take
zata fada maka man lita nawa ne, sannan zata fada
maka man tafiyar mita nawa zaiyi ya kare.
Nuna Maka Wanda Ya Kira Ka Koda Kuwa Ba An Boye Lambar: Da wayar android zaka san daga
inda wani ya kiraka ko missed call, ko lambar ba
suna ko an boyeta (Private Number) ,to za kayi
amfani da wani application wanda yana amfani da
network din lambar da aka kira ka da Zip code na
jiha, da kuma Postal code na Local Govt. Sannan ya nuno maka guri na wanda ya kira a jikin map da
sunan yankin.
Nuna Maka Hanya: Da wayar android zakayi tafiya
zuwa Abuja, amma baka san hanya ba to za kayi
amfani da wani application shi zai nuna maka
tunda ga inda kake har zuwa cikin Abuja, kuma ana saitawa ta yadda idan ka kauce daga kan
hanya zai maka alert da cewa kabar hanya.
Kulle Wayar Android:
Da wayar android zaka kule wayar abokinka ko
wani ma can,sannan kuma wani zai iya kulle
wayarka cikin sauki, ta hanyar turo maka sakon SMS ta cikin layinsa.misali ni wizard ina funtua zan
iya kulle wayarka kai da kake kano ta hanyar turo
maka da sakon MAGIC SMS.
Auna Data:
Da wayar android zaka san adadin MB din da kayi
amfani da ita a duk wata ko sati, kuma zata fada maka 10MB awa nawa zatayi ko minti, amma idan
bakayi download ba.
Koyon Maths.
A cikin wayar android zaka san duk wata formular
ta maths, da yadda ake bi domin sarrafata.
Daukar Videos Din Hanya: Da wayar android zaka tafiya daga nan funtua
zuwa Kano state,to sai kayi amfani da wani
application domin yayi maka video na hanyar daka
bi, shi kuma videon hanyar da kake dauka wannan
app din zai ware duk abinda aka dauka na shirme
zai ajiye muhimmai na daga abinda ya faru a hanya su kawai zaima save nasu,idan ka sauka saika
kunna ka kalli abinka.
Editing Na Videos:
Da wayar android xaka iya yin editing na videos
din da kakeso kuma sanya hotunan da kake so
aciki ko ka jona videos da kakeso da taimakon wani app wanda nike amfani dashi domin gyara
videos din film din da nike producing a garinmu in
sanya taken lamba,ka yanke inda bana so a ciki ko
gyara inda nikeso.
Android A Matsayin Modem Ta Computer:
Zaka iya amfani da wayar android ka hada ta da computer ka ta zama kamar modem kayi browsing
da ita a matsayin modem a PC.
Kai akwai abubuwa da dama wadanda bazan iya
zaiyana su anan ba duka na abubuwan da wayar
android keyi.
Bisssalam Allah yabada Sa a Allah yasa kowa ya fahimta
0 Comments