Aslm yan'uwa maza da mata mabiya wannan Shafi mai albarka, Darasinmu nayau zamuyi magana ne akan
{{ ROOTING }}
- MENENE ROOTING Rooting wata hanyace ta karawa wayoyi ko tablet din android karfin aiki ta hanyar ninka gudunta da kara mata fikirori.
- MENENE YASA KI/KAKESON YIN ROOTING Abubuwan da zasu saka ka/Ki rooting shine
- Rooting ze baka daman using VPN
service wanda shi aikin VPN shine ya boye ip address dinka ta yadda idan kana
Nigeria kana browsing, ze riqa nunawa Kaman kana wani qasa ne can waje, kuma idan akwai restrictions misali
Kaman MTN to VPN din ze hana mtn blocking dinka… (Har Free Browsing zaka iya yi idan kayi rooting)
- ka cire guarantee din wayarka ko kuma ka lalata wayarka a wajanyi
Cire guarantee, kamfanoni suna cewa in kai rooting ka cire guarantee da suka baka, Saboda duk wani shinge da suka saka ka tsallake shi Amma ka Sani in ka bukaci cire rooting zaka iya cirewa duk sanda ka so. Kaga wannan Ba matsala Ba ne.
Lalata waya. A kan samu tsautsayin lalacewar waya yayin rooting Amma Sai in Ba abi hanyar yin rooting din dai dai Ba in kabi hanya dai dai zakai cikin Nasara ka Gama Ba matsala Dan haka ka tabbata ka Bi hanyar da ta dace. - KUMA DOLENE SE NAYI ROOTING NA WAYANA ANDROID?
Amsa —> A’a ba dole bane kayi rooting wayar ka ta android idan kai ba irin mutanan da suke rike waya don karantar ita kanta
wayar da sirrukanta ta inda duk wata matsala zaka iya
sanin dalilin ta ba… Idan burin ka shine kaga
ka riqe wayan kana kira, koka hau 2go ko
fb, ko kayi chatting a whatsapp, ko kallon
videos da daukan hoto to baka da buqatan rootin.
Amma idan kai burin ka
ka cika wayar da application ne kuma kai
ma,abocin browsing ne da son ganin kana
upgrading version din android dinka
Kaman yadda masu bb sukeyi, ko ka canza ma wayar fasali ta yadda wani can me irin wayar ka zeyi mamakin ganin
naka domin banbancin su a application to
kana buqatar rooting.
Rooting kamar jailbreak ne a iPhone ko hack ne symbian ga Wanda yayi amfani da wayar iPhone ko symbian a baya, Kuma Yana Ba masu amfani da waya damar chanja ainihin kwakwalwarta, hasali ma Yana bada damar chanja komai na waya zuwa yadda ake so. Da rooting zaka tsallake duk wani shinge da kamfanin da suka kera wayarka suka Sama Dan ragewa wayarka dadin amfani. Zaka sa applications masu matukar yawa da amfani,rage ko kara saurin wayar kai hatta da shi android system din zaka iya sa sabon da Google suka Saki ko kamayar da shi karami Wanda kake so ma'ana kana da yanci akan wayarka.
Domin sanin yadda akeyin rooting sai Ku karanta darasinmu Na gaba me muna { YADDA AKEYIN ROOTING DALLA-DALLA } Akwai cikakken bayani akan yadda ake rooting,a darasin akwai screenshot domin Ku fahimta yadda ya kamata
MUN GODE
1 Comments