YADDA AKEYIN ROOTING DALLA-DALLA, CIGABAN DARASIN ROOTING









Aslm yan uwa maza da mata, mabiya wannan shafi namu me Albarka, yau zamu cigaba da darasinmu akan

{ ROOTING }

Idan me karatu yana biye damu a darasinmu daya gabata munyi magana ne akan Rooting, muna fatan kun karanta kuma kun fahimta, ga Wanda basu karantaba shiganan domin karantawa MENENE ROOTING, MAYE AMFANINSA

To yanzu zamu dora a inda muka tsaya.

YA AKE YIN ROOTING

Da farko muna da hanyoyi har guda biyu, da ake bi domin yin rooting
  1. Computer
  2. Phone
Yanzu zamuyi maganane akan yadda akeyin da phone


Zamu iyayin amfani da wayarmu wajan gudanar da wannan Aiki ta hanyar amfani da wasu application, daban daban amma zabina a gareku shine wannan

kingroot yana da Kyau kuma da saukin amfani domin nima dashi nayi na wayata, fa farko kuyi download Na wannan application zaku sameshi anan DOWNLOAD KINGROOT
ko Kuje ( playstore ) kuyi download Na wannan application , bayan kunyi installed sai open bayan ya bude Zai baku fili kamar haka



sai kudannan start root daganan zaku Dan jira,bayan ya gama shikenan Root successful
.Gashi kamar haka



Fatan kunji dadin wannan darasinmu mu hadu a darasi na gaba MUN GODE


Naku harkullum Ibrahim kodamekazognm


Domin tambaya da Karin bayani sai kuyi comment. 09067511839 kira ko WhatsApp Na gode







Post a Comment

0 Comments